Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bukaci Musulmi da su yi amfani da bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW) wajen tunani da kuma aiwatar da koyarwarsa ta hadin kai, tausayi da zaman lafiya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna da ya aika wa Musulmi a jihar Bayelsa da sauran sassan Najeriya yayin bikin Eid-el-Maulud.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Daniel Alabrah, ya fitar a ranar Talata, Diri ya ce Mauludi lokaci ne na tunawa da soyayya da kuma kyawawan dabi'un sadaukarwa.
Ya bukaci Musulmi su nuna soyayya a aikace, su kasance masu taimakon juna tare da kokarin tabbatar da zaman lafiya da kyakkyawar mu'amala a tsakanin al'umma.
Gwamnan ya ce koyarwar Annabi Muhammad (SAW) kan soyayya, hadin kai, tausayi da zaman lafiya na bukatar a yi amfani da ita wajen gina al'umma mai hadin kai.
Diri ya kuma taya Musulmin jihar Bayelsa da Najeriya baki daya murnar bikin Mauludi, tare da yi musu fatan samun karin wadata, farin ciki da zaman lafiya.
Ya ce, “Ina taya 'yan uwana Musulmi murnar wannan biki na Maulud. Allah Ya sa bikin ya kawo karin ci gaba da farin ciki gare ku da jiharmu baki daya. Barka da Maulidi.”