Lokacin da aka tambayi tsohon kocin Liverpool, Rafael Benitez, ko ya taɓa tunanin cewa tsoffin ‘yan wasansa, Xabi Alonso da Alvaro Arbeloa, za su zama masu horar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, amsarsa ta kasance kai tsaye.
“Alonso, eh. Arbeloa kuwa, ba sosai ba,” in ji Benitez. “A gare ni, Arbeloa ya ba ni mamaki.”
Kusan shekaru 20 bayan da Benitez ya haɗa su a Liverpool, yanzu tsoffin abokan wasan biyu za su fafata a matsayin masu horarwa, yayin da Fulham da Arbeloa ke jagoranta za ta karɓi baƙuncin Chelsea ta Alonso a yau Litinin.
Alonso da Arbeloa sun lashe gasar cin kofin duniya ta 2010 tare da tawagar Spain, baya ga lashe gasar cin kofin nahiyar Turai sau biyu.
Haka kuma, sun samu nasarori a gasar La Liga da sauran kofunan cikin gida bayan da suka koma Real Madrid daga Liverpool.
Sun shafe shekaru bakwai suna buga wasa tare a matakin kulob, inda suka kasance tare a fili sau 262 a wasannin kulob da na ƙasa.
Tun bayan da suka yi ritaya daga buga ƙwallo, hanyoyin aikinsu a fagen horarwa sun ci gaba da kasancewa a haɗe.
Arbeloa ya samu damar ɗaukar nauyin babban ƙungiyar Real Madrid bayan an ɗaga shi daga Real Madrid B, Castilla, domin maye gurbin Alonso bayan da aka sallami Alonso daga jagorancin katafaren kulob ɗin na Spain a watan Janairun bara.
Yanzu, tsoffin abokan wasan za su fuskanci juna a matsayin masu horarwa, a wani sabon babi na tarihin ƙawancensu da suka fara tun lokacin da suke buga wasa tare a Liverpool.