Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), reshen Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya buƙaci Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da ya tabbatar da adalci da gaskiya ga dukkan ‘yan ƙasar ba tare da la’akari da addininsu ko jam’iyyar siyasar da suke goyon baya ba.
Jingir ya bayyana hakan ne a wani taron ƙasa mai taken “Inganta Harkokin Siyasa da Adalci a Matsayin Hanyar Samar da Haɗin Kai da Ci Gaba a Najeriya”, wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Sadeeqa da ke Jos, Jihar Plateau.
Malamin ya ce goyon bayansa ga tsarin tikitin shugaban ƙasa da mataimakinsa waɗanda dukkaninsu Musulmai ne, ba yana nufin yana ƙin Kiristoci ko sauran ‘yan Najeriya da ba Musulmai ba.
Ya ce matsayinsa na siyasa bai samo asali daga ƙiyayya ko kyamar wani addini ba.
Sheikh Jingir ya kuma yi kira ga Shugaba Tinubu da kada gwamnatinsa ta nuna wariya ga waɗanda ba Musulmai ba ko kuma ‘yan Najeriya da ba sa cikin jam’iyyar APC.
Ya jaddada cewa shugaban ƙasa yana da alhakin tafiyar da mulki bisa adalci da gaskiya, tare da tabbatar da cewa kowane ɗan ƙasa yana samun hakkinsa.
A cewar Jingir, kowane ɗan Najeriya yana da ‘yancin zaɓar ɗan takarar da yake ganin ya dace da shi a lokacin zaɓe, ba tare da tilasta masa yin la’akari da addinin ɗan takarar ba.
Ya bayyana cewa shi kansa ya taɓa goyon bayan wani ɗan takarar gwamna Kirista a Jihar Plateau, inda ya ce babban abin da ya yi la’akari da shi shi ne wanda zai iya tabbatar da adalci da kuma wakilcin Musulmi da sauran al’umma a cikin gwamnati.
Da yake magana kan zaɓen gwamnan Jihar Plateau na shekarar 2007, Jingir ya ce ya ƙi goyon bayan wani ɗan takarar Kirista ne bayan ya lura cewa babu wani Musulmi a cikin tawagar da ta raka ɗan takarar wajen neman goyon bayansa.
A cewarsa, lamarin ya ƙara tabbatar masa da cewa adalci, wakilci da kare muradun al’umma su ne abubuwan da ya kamata su zama tushen zaɓin siyasa, ba ƙiyayya ko bambancin addini ba.
Sheikh Jingir ya ce shugabanni ya kamata su tabbatar da cewa dukkan ‘yan Najeriya suna da matsayi da dama iri ɗaya a ƙarƙashin gwamnati, ba tare da nuna bambanci saboda addini ko siyasa ba.