Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Domin Inganta Kula da Lafiyar Masu Rauni
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da abokan hulɗa domin inganta kiwon lafiya da tallafa wa ’yan Najeriya masu rauni , musamman mutanen da ke rayuwa da nakasa. Ministan da ke Kula da Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate , ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai al’ummar Karon Majigi da ke kan titin Airport Road a Abuja, inda ya duba yanayin rayuwa da buƙatun kiwon lafiya na mutanen da ke da nakasa. Daga cikin mutanen da ya ziyarta akwai masu matsalar gani, waɗanda aka yanke wa gaɓoɓi, da mutanen da cutar shan inna da kuturta ta shafa . Ministan ya
