Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu , ya jagoranci manyan jami’an tsaro daga Najeriya zuwa birnin Washington, D.C. , domin halartar babban taron Ƙungiyar Aiki ta Haɗin Gwiwa Najeriya da Amurka kan harkokin tsaro.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci , duba ci gaban da aka samu zuwa yanzu, da kuma gano sabbin hanyoyin da za a zurfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.
Daga cikin manyan jami’an tsaron Najeriya da ke cikin tawagar akwai Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu .
Ana sa ran tattaunawar za ta ƙara inganta musayar bayanan sirri, haɗin gwiwar yaki da ta’addanci da kuma sauran ƙalubalen tsaro da ƙasashen biyu ke fuskanta.
