Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso , ya ce wasu kalaman malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir , na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Najeriya.

A wata sanarwa da Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana damuwarsa kan kalaman Sheikh Jingir da ya yi a wani taro a Kano a ƙarshen mako.

Kwankwaso ya jaddada cewa al’ummar Kano ba sa goyon bayan kalaman da za su iya raba kan ’yan Najeriya , yana mai cewa bai kamata a yi amfani da murya ko matsayi wajen furta kalaman da za su raunana haɗin kan ƙasa ba.

A kwanakin baya ne kafafen sada zumunta da na yaɗa labarai suka ɗauki zafi sakamakon cece-kuce kan kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙungiyar Izala, dangane da batun Muslim-Muslim .

Kwankwaso, wanda shi ne mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC , Peter Obi, ya ce abin damuwa ne yadda irin waɗannan kalamai ke fitowa daga bakin malamin addini da ke da matsayi da tasiri a tsakanin al’umma.

Ya ce: “Bai kamata mu yi amfani da muryarmu wajen faɗin kalaman da za su iya raunana haɗin kan ƙasarmu ba.”

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa, a wannan lokaci da Najeriya ke ciki, ya kamata a yi watsi da duk wasu kalamai ko ayyukan da ka iya haifar da rashin haɗin kai tsakanin al’ummar ƙasar.