Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da cewa an kashe ’yan bindiga 17 da ake zargi a wata arangamar musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Sakaba ta jihar Kebbi .

Rundunar ta kuma ce wasu daga cikin jami’anta da fararen hula biyu sun rasa rayukansu yayin arangamar.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:25 na safiyar Litinin , a yankin Rafin Makuku na Sakaba , lokacin da jami’an ’yan sanda suka tare wasu da ake zargin ’yan bindiga ne yayin da suke ƙoƙarin ratsa yankin tsakanin jihohin Zamfara da Kebbi .

Rundunar ta ce an kuma lalata babura huɗu da ake zargin maharan ne suka yi amfani da su.

Haka kuma, wasu jami’an ’yan sanda biyu sun samu raunuka kuma a halin yanzu suna karɓar magani.

An kai gawarwakin jami’an da suka mutu zuwa Birnin Kebbi , yayin da aka ƙara tura wasu jami’an tsaro zuwa yankin domin ci gaba da ayyukan dakile ayyukan ’yan bindiga da tabbatar da tsaron al’umma.