Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf , ya amince da ƙarin albashi ga malamai da sauran ma’aikatan jami’o’in jihar.
Ƙarin albashin zai shafi Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil da kuma Jami’ar Northwest .
Gwamnan ya amince da matakin ne bayan wani kwamiti da Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta kafa ya duba buƙatar jami’o’in biyu na shigar da sabon tsarin albashin cikin tsarin jihar.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa , ya fitar ranar Litinin, sabon tsarin albashin ya fara aiki tun daga Janairun 2026 , yayin da za a fara biyan ƙarin kuɗin daga Satumban 2026 .
Sanarwar ta ce ƙarin albashin jami’o’in biyu zai ci wa gwamnatin jihar kusan naira miliyan 391.8 duk wata , wanda ya haura naira biliyan 4.7 a shekara .
Gwamnatin jihar ta ce matakin ya biyo bayan sabon tsarin albashin da gwamnatin tarayya ta fara amfani da shi a jami’o’in gwamnatin tarayya, da nufin inganta jin daɗin ma’aikatan jami’o’i da ƙarfafa harkokin ilimi.
