AMMASCO RADIO NEWSROOM

politics

Tinubu Ya Karɓi Daftarin Kasafin Kuɗin MDD na 2027

Wakilin dindindin na Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce karɓar daftarin kasafin kuɗin ya zama tarihi, yana mai cewa shi ne karo na farko cikin shekaru 66 da shugaban ƙasar ya karɓi irin wannan takarda.

APC Ta Musanta Zargin Shirin Kashe Atiku Abubakar

Jam’iyyar APC ta ce ba ta da hannu a duk wani shiri na cutar da Atiku Abubakar, tare da kira ga Timi Frank da ya miƙa hujjojinsa ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike.

Jihohi 12 da Tinubu zai ziyarta a yaƙin neman zaɓen 2027

Shugaba Bola Tinubu zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓen sake zaɓensa a jihohi 12 na Nijeriya gabanin zaɓen 2027, yayin da shugabannin jam’iyyar APC za su wakilce shi a sauran jihohin ƙasar.

Kungiyar mata Musulmi ta Arewa ta goyi bayan Tinubu a zaben 2027

Akalla mata Musulmi 500 da suka hada da malamai, masu wa’azi da shugabannin Da’awah daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja, sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2027. Matan sun bayyana matsayinsu ne a karkashin kungiyar Muslim Intellectuals Forum , yayin wani taron tuntuba da aka gudanar a Kaduna ranar Lahadi. A cewarsu, sun yanke wannan shawara ne bisa la’akari da nasarorin da suka ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta samu tun bayan hawanta kan mulki. Sun ambaci bangarorin ilimi, tsaro, samar da ababen more rayuwa da

INEC ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu na zaben 2027

Jerin sunayen wanda Sakatariyar Hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, an fitar da shi ranar Asabar a Abuja wanda ya ƙunshi ’yan takara da jam’iyyun siyasa 18 suka tsayar domin neman kujerar shugaban ƙasa. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa daga cikin ’yan takarar shugaban ƙasa 18, 16 maza ne, wanda ya kai kashi 88.9 cikin 100, yayin da biyu mata ne. NAN ta kuma ruwaito cewa maza da ke cikin jerin Yan takarar sun haɗa da Bola Tinubu na APC, Abubakar Atiku na Jam'iyar ADC, da Peter Obi na NDC. Sauran sun haɗa da Adewole Adebayo na Social Democratic Party (SDP),

Gwamnan Katsina ya gabatar da kasafin kuɗin N828.64bn na 2027 ga majalisar dokokin jihar

Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda ya gabatarwa majalisar dokokin jihar da daftarin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2027 , wanda ya kai Naira biliyan 828.64 a ranar talata domin amincewa. Kusan kashi 77 cikin 100 na kasafin kuɗin an ware shi ne domin ayyukan raya ƙasa. Kasafin kuɗin mi taken “Building Your Future IV” , ya ware Naira biliyan 637.91 , wato kashi 76.98 cikin 100 , domin ayyukan manyan ayyuka, yayin da aka ware Naira biliyan 190.73 , kwatankwacin kashi 23.02 cikin 100 , domin gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnati. Adadin kasafin kudin ya ragu da Naira biliyan 69.23 idan aka

INEC ta fitar da Jerin sunayen mutane 12 dake neman takarar kujerar Gwamnan jihar Kwara a zaben 2027

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta bayyana sunayen ’yan takarar kujerar gwamnan Jihar Kwara guda 12 da mataimakansu, domin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027. Hakan ya ya baiwa Yan takarar damar fara shirye-shiryen yakin neman zabe gabanin babban zaɓen ƙasa. INEC ta bayyana jerin sunayen ne a ofishin hukumar da ke Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, a ranar Asabar, inda ’yan takarar suka fito daga jam’iyyun siyasa daban-daban. Hukumar ta bayyana Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Yakubu Danladi-Salihu, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, yayin da Bello

Siyasa ce kawai tasa Atiku furta dawo da tallafin manfetur, amma abune da bazai iya ba - cewar gwamnatin tarama

Gwmnatin Tarraya ta ce tufka da warwarar da jagoran ‘yan adawa kuma ɗantakaran jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ke yi kan batun mayar da tallafin mai na nuna cewa siyasa kawai ne yake son yi da batun mayar da tallafin. A wata sanarwar da ya fitar jiya Laraba babban mai bai wa Shugaban Tinubu Shawara kan Watsa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya ce sauya maganar da Atiku ya yi sau uku cikin mako ɗaya ya nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar siyasa kawai yake yi da batun dawo da tallafin mai. Sanarwar ta ce daga farko mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya ce Atiku zai mayar da tallafi idan

kungiyar Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027, tayi barazanar dai na tallata Tinubu idan ba a cire Sharif daga Kwamitin kamfe ba

Wata kungiyar magoya bayan APC da ke yakin neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ta yi barazanar janye goyon bayan da take ba shi bisa radin kanta, idan har tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ci gaba da kasancewa cikin tsarin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC. Kungiyar mai suna Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027, ta bayyana wannan gargadi ne cikin wata takardar korafi mai dauke da kwanan watan 25 ga Agusta, 2026, wadda ta aika wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, tare da kwafin takardar zuwa fadar shugaban kasa. Kungiyar t

Kwamishinan Yansandan Abuja ya gargadi DPOs da Kada su kuskura su tsare mutum Sama da awa 24 ba tare da izinin kotu ba

Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT), CP Ahmed Mohammed Sanusi, ya gargadi Jami’an ’Yan Sanda Masu Kula da Rukunan ’Yan Sanda (DPOs) da kada su tsare waɗanda ake zargi na tsawon fiye da sa’o’i 24 ba tare da ingantaccen umarnin kotu ko wata sahihiyar izini ta doka ba. Sanusi ya bayar da wannan umarni ne a yayin wata ziyarar sa ido da ya kai ga Rukunin Yankunan Metro da Life Camp, inda ya duba ayyukan gudanar da aiki tare da tantance yadda jami’an ke gudanar da ayyukansu da kuma irin rawar da suke takawa. Musamman, ya gargadi jami’an da ke sassan ’yan sandan birnin Abuja kan tsare

Tsahon Gwamnan gombe Goje, ya bayyana cewa Har yanzu shi mamba ne na APC, Amma nan ba da jimawa ba zai bayyana matakin makomar tafiyar siyasarsa

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe kuma Sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya bayyana cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar mutane da kuma yin shawarwari kan makomarsa ta siyasa. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugabannin siyasa daga jam’iyyun PDP da ADC suna kokarin jawo Sanata Goje zuwa jam’iyyunsu, tare da matsa masa lamba ya sauya sheka, bayan da ya bayyana cewa APC ba za ta ba shi tikitin takara ba. Da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa a gidansa da ke Gombe ranar Asabar, Goje ya musanta cewa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyyar siyasa, inda ya tabbatar da cewa

KWANKWASO YA NEMI BINCIKE KAN HATSARIN KWALWALEN SOKOTO

Tsohon Gwamnan Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Rabiu Kwankwaso , ya jajanta wa iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwale da ya afku a Gorau, ƙaramar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto. Kwankwaso ya bayyana hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a matsayin babban abin takaici, yana mai kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin. A cewar rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto, mutane 77 ne ke cikin kwale-kwalen da ya kife yayin da yake ɗauke da manoma da sauran fasinjoji zuwa gonakins

INEC ta bai wa Adeleke takardar nasara a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Osun

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya ( INEC ) ta bai wa Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke , da mataimakinsa, Kola Adewusi , takardun shaidar nasara bayan lashe zaɓen Gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta 2026 . An gabatar da takardun shaidar nasarar ne a hedikwatar INEC ta jihar da ke Osogbo , inda Kwamishinan Ƙasa na INEC mai kula da Jihar Osun, Farfesa Yinka Ajayi , ya jagoranci bikin. Gabatar da takardun ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Osun , yayin da Kola Adewusi ya zama zaɓaɓɓen mataimakin gwamna.

APM ta lashe kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 20 a Bauchi

Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta lashe dukkan kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 20 a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a faɗin Jihar Bauchi ranar Litinin. Shugabar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi (BSIEC), Jummai Abubakar, ce ta bayyana sakamakon zaɓen. Ta ce baya ga kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 20, jam’iyyar APM ta kuma lashe kujerun kansiloli 319 daga cikin 323 da aka fafata a jihar. Rahotanni sun ce wasu daga cikin jam’iyyun adawa sun kaurace wa zaɓen, lamarin da ya bai wa APM damar lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomin jihar.

Jam'iyar APM ta cinye zaben kujerun Kananan hukumomi 20 na Jihar Bauhci

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC) ta bayyana cewa APM ta kuma lashe kujerun kansiloli 319 daga cikin 323. Shugabar hukumar, Jummai Abubakar, ta ce dukkan ‘yan takarar APM 20 sun samu nasara bayan kammala kada kuri’a, kirga kuri’u da tattara sakamako. Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya soki jam’iyyun adawa kan kaurace wa zaben, yana mai cewa sun yi hakan ne saboda tsoron faduwa. Gwamnan ya bayyana zaben a matsayin wanda aka gudanar cikin kwanciyar hankali, tare da jaddada muhimmancin kananan hukumomi wajen samar da ci gaba da kyakkyawan shugabanci.

. Ayyukan Tinubu sun nuna cancantar sake zaɓensa a 2027 – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci a sake zaɓensa a shekarar 2027, bisa la’akari da sauye-sauyen tattalin arziki da ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta aiwatar. Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Ayyuka na Musamman, Tunde Rahman , ne ya bayyana hakan yayin wani rangadin ayyukan gwamnati a Jihar Nasarawa. Ayyukan Raya Ƙasa Rahman ya ce ayyukan tituna, gadoji da cibiyoyin lafiya da tawagar ta gani a Nasarawa da Benue na daga cikin nasarorin da aka samu sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar. Ya ƙara da cewa sauye-sauyen g