Akalla mata Musulmi 500 da suka hada da malamai, masu wa’azi da shugabannin Da’awah daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja, sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2027.

Matan sun bayyana matsayinsu ne a karkashin kungiyar Muslim Intellectuals Forum , yayin wani taron tuntuba da aka gudanar a Kaduna ranar Lahadi.

A cewarsu, sun yanke wannan shawara ne bisa la’akari da nasarorin da suka ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta samu tun bayan hawanta kan mulki.

Sun ambaci bangarorin ilimi, tsaro, samar da ababen more rayuwa da bunkasar tattalin arziki a matsayin wasu daga cikin abubuwan da suka yi la’akari da su wajen bayyana goyon bayansu.

Sanarwar goyon bayan ta kunshi wani kuduri da Aisha Iliyasu Tukur daga Jihar Jigawa ta karanta a karshen taron.

Kungiyar ta ce tana ganin ci gaba da mulkin Shugaba Tinubu zai taimaka wajen dorewar wasu daga cikin manufofi da shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta fara aiwatarwa.

Matsayar kungiyar na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa da kungiyoyi daban-daban ke kara shirye-shiryen tunkarar babban zaben shekarar 2027