ojojin sun hallaka yan ta'adda 6 tare da kwato shanun da aka sace a Lakwaya da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo a nan Kano. 

Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran ƙaramar hukumar Gwarzo, Auwalu Musa Yola, ya fitar yau Laraba.

Ya ce, lamarin ya faru ne yayin wani sumame da jami’an tsaron suka gudanar a yankin Lakwaya, inda suka tunkari ’yan bindigar.

Sanarwar ta ce, Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwarzo, Hon. Mani Tsoho, ya ziyarci yankin na Lakwaya domin yaba wa jami’an tsaro kan matakin.

Shugaban ya buƙaci al’ummar yankin da su ci gaba da taka tsantsan tare da isar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro cikin gaggawa domin taimaka musu wajen dakile ayyukan ’yan bindiga.