Gwamnatin Jigawa ta amince da ware Naira biliyan 12.68 domin gina sababbin gine-gine, samar da kayan aiki da gyara wasu makarantun sakandare sama da 50 a faɗin jihar.

A cewar gwamnatin jihar, aikin zai shafi makarantun sakandare da ke sassa daban-daban na Jigawa, kuma an tsara shi ne domin magance ƙarancin kayayyakin more rayuwa a makarantu tare da inganta yanayin karatu ga ɗalibai da aikin koyarwa ga malamai.

Ayyukan sun haɗa da gina sababbin gine-ginen makarantu, samar da kayan aiki da gyaran wasu gine-ginen da ake da su.

Gwamnatin ta ce zuba jarin zai taimaka wajen rage cunkoso da matsin lamba kan kayayyakin makarantu, domin ɗalibai su samu damar yin karatu a wuraren da suka dace.

A cewar gwamnatin, inganta ilimi na daga cikin muhimman abubuwan da aka sanya a cikin Ajandar Maki 12 ta gwamnatin jihar.