Wike ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyar siyasarsa ta Rainbow Coalition.

Taron, wanda ya gudana ranar Litinin, ya samu halartar sarakunan gargajiya, jiga-jigan siyasa da mazauna yankin Ƙaramar Hukumar Kwali.

Ministan ya buƙaci kansilolin da su nemi goyon bayan mazauna yankunansu da ƙungiyoyin al’umma domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a mazaɓunsu, kamar yadda tashar Channels Television ta ruwaito.

“Duk kansilan da ya kawo wa Tinubu nasara a mazaɓarsa zai samu kyautar naira miliyan 10. Don haka ku je ku gana da shugabanninku, ku gana da ƙungiyoyin matasa, ku tattauna da ƙungiyoyi daban-daban. Mu tabbatar da mun samar wa Shugaban Ƙasa nasara a mazaɓunmu,” in ji Wike.