Lamola ya bayyana hakan ne a cewar rahotannin gidan talabijin na ƙasar, SABC, bayan taƙaddamar da ta samo asali daga abin da ya faru a bikin miƙa takardun kama aiki na sabbin jakadu ga Shugaba Cyril Ramaphosa.
Fadar Pretoria ta yi sammacin jakadan Najeriya, Femi Fani-Kayode, bayan taƙaddamar da ta samo asali daga bikin da Ramaphosa ya karɓi baƙuncin sabbin jakadu domin su miƙa takardun kama aiki.
A ranar 17 ga Nuwamban 2026, Fani-Kayode ya gana da Babban Daraktan Harkokin Ƙasashen Waje da Haɗin-gwiwa na Afirka ta Kudu, Zane Dangor, wanda ya isar da damuwar gwamnati kan wasu wallafe-wallafen jakadan a shafukan sada zumunta game da bikin a fadar shugaban ƙasar.
Yayin ganawar, Dangor ya tunatar da jakadan game da Yarjejeniyar Vienna kan mu'amalolin diflomasiyya, wadda ke buƙatar jakadu su gudanar da harkokinsu ta hanyoyin diflomasiyya da aka amince da su.
Ganawar ta kasance mai faram-faram
Daga bisani, Fani-Kayode ya bayyana ganawar a matsayin mai faram-faram kuma mai cike da alfanu, inda ya ce ƙasashen biyu suna ci gaba da nuna aniyarsu ta ƙarfafa dangantakarsu mai tarihi.
Amma mene ne takamammen abin da ya haddasa taƙaddamar tsakanin ƙasashen biyu mafiya ƙarfin tattalin arziki a Afirka?
Taƙaddamar ta fara ne ranar Juma'a, 13 ga Nuwamban 2026, lokacin da Ramaphosa ya karɓi takardun sabbin jakadu 15 da aka aika Pretoria.
Fani-Kayode, wanda shi ne cikakken jakadan Najeriya na farko da aka aika Afirka ta Kudu cikin kusan shekaru huɗu, ya zargi fadar shugaban ƙasar da katse jawabinsa na gabatarwa da gangan a cikin bidiyon bikin da aka watsa kai-tsaye.
Ya yi tambaya kan dalilin da ya sa ba a cire jawaban sauran jakadu 14 daga bidiyon ba, amma aka cire nasa.
Fani-Kayode shi ne na ƙarshe cikin jakadun da suka gabatar da jawabai, kuma jami'an Afirka ta Kudu sun ce tangarɗar na'ura ce ta haifar da katsewar.
Babu katsewa da gangan
Fadar shugaban ƙasar Afirka ta Kudu ta yi watsi da iƙirarin cewa an katse jawabin jakadan Najeriya da gangan.
Kakakin fadar shugaban ƙasar, Vincent Magwenya, ya ce Ramaphosa ba shi da ikon katsalandan a hukuncin editocin kafar yaɗa labaran gwamnati, ciki har da SABC.
SABC ma ta fayyace cewa ɗaukar bidiyon bikin wani batu ne daban da shirye-shiryen watsa bikin fadar shugaban ƙasar.
Daga baya, fadar shugaban ƙasar ta wallafa cikakken bidiyon bikin a YouTube.
Sai dai lamarin ya haddasa muhawara tare da rura wutar taƙaddamar da ake yawan samu tsakanin ƙasashen biyu.
Haramta baƙin haure
A watan Yuni da Yulin 2026, zanga-zangar adawa da ƴan ƙasashen waje da kasuwancinsu a Afirka ta Kudu ta janyo Najeriya ta ƙaddamar da shirin kwashe ƴan ƙasarta kusan 1,500.
Sauran ƙasashen Afirka da dama sun ɗauki irin wannan mataki bayan tashin hankalin zanga-zangar ƙyamar baƙin haure.
Duk da taƙaddamar, Najeriya da Afirka ta Kudu, waɗanda ke cikin ƙasashen Afirka mafiya ƙarfin tattalin arziki, suna da alaƙar tarihi mai zurfi.
Najeriya ta ba Afirka ta Kudu babbar gudunmawa a fafutukar yaƙi da mulkin wariyar launin fata na apartheid, inda ta samar da tallafin kuɗi da na diflomasiyya ga ƙungiyoyin neman 'yanci.
Tun bayan ƙarshen apartheid a 1994, ƙasashen biyu sun gina alaƙar siyasa da tattalin arziki, inda Najeriya ta zama babbar abokiyar cinikayyar Afirka ta Kudu a nahiyar Afirka, duk da cewa suna samun saɓani lokaci-lokaci.
A yanzu dai, gwamnatocin ƙasashen biyu sun jaddada aniyarsu ta girmama juna da ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninsu.
