Rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga ne suka kashe mutanen biyu a wani hari da suka kai musu a cikin mota a yammacin ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Tinubu ya bayyana alhininsa kan kisan, yana mai cewa irin wannan aika-aika ta saɓa wa ƙimar zaman lafiya da kuma tsarkin rayuwar ɗan Adam.

Shugaban ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, mabiyansu, da gwamnatin Jihar Katsina, tare da al’ummar jihar baki ɗaya bisa wannan babban rashi.

Tinubu ya kuma umarci rundunar ’yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa da su ƙarfafa binciken da ’yan sandan Jihar Katsina suka fara, domin gano waɗanda ake zargi da aikata kisan, a kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Shugaban ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamatan, Ya gafarta musu, sannan Ya ba iyalansu da duk waɗanda ke makokin rasuwarsu haƙurin jure wannan rashi.