A ranar Laraba ne Mai Martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ya naɗa Seyi Tinubu wannan sarauta a fadarsa.

A cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, Bola Tinubu ya nuna godiyarsa ga Sarkin Gwandu da Majalisar Masarautar bisa wannan karramawa, wadda a cewar Sarkin ita ce irinta ta farko a tarihin masarautar.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa wannan karramawa ba wai girmama mutum ɗaya kawai take nufi ba, tana kuma nuna abota, mutunta juna da haɗin kai tsakanin al'ummomin Najeriya.

Ya ce a matsayinsa na uba, yana farin cikin ganin wata fitacciyar masarauta mai dogon tarihi ta karrama ɗansa.

Haka kuma, shugaban ya yaba da ƙoƙarin Seyi Tinubu wajen hulɗa da matasa, bunƙasa al'umma da ƙarfafa gwiwar jama'a, musamman ta hanyar ƙungiyar City Boy Movement da sauran shirye-shiryen tallafa wa matasan Najeriya.

Tinubu ya kuma buƙaci ɗansa da ya kasance mai tawali'u, tare da gudanar da rayuwarsa bisa darajojin jarumtaka, shugabanci da hidimar al'umma waɗanda wannan sarauta ke wakilta.

Ya ƙara da cewa ya kamata Seyi ya ɗauki wannan sarauta a matsayin ƙarin nauyi da kira na bayar da gudummawa wajen tabbatar da ci gaba, zaman lafiya da yi wa Najeriya hidima.