Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar buƙatar shugaban ƙasar yayin zaman majalisar a ranar Talata.

A cikin wasiƙar, Tinubu ya bayyana cewa rancen ya zama wajibi domin bai wa gwamnatin tarayya damar sauke nauyin da ke kanta ga ’yan Najeriya da kuma samar da kuɗaɗen gudanar da ayyuka a muhimman fannoni.

Shugaban ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta duba shirin tare da amince da shi cikin gaggawa, domin a fara aiwatar da ayyukan da aka tsara ba tare da ɓata lokaci ba.

Ya bayyana cewa an tsara ayyukan da ke cikin shirin ne bisa ƙididdigar fasaha da nazarin tattalin arziƙi, tare da la’akari da gudummawar da ake sa ran za su bayar wajen bunƙasa zamantakewa da tattalin arziƙin ƙasar.

A cewarsa, ayyukan za su mayar da hankali kan samar da ayyukan yi, bunƙasa koyon sana’o’i da kasuwanci, rage talauci da kuma inganta wadatar abinci a Najeriya.

Majalisar Dattawa Za Ta Nazarci Buƙatar

A nasa ɓangaren, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce an riga an tattauna wasu sassan shirin rancen a baya yayin nazarin kasafin kuɗi, sannan majalisar ta amince da wani shirin rancen kuɗin waje a wani lokaci da ya gabata.

Akpabio ya miƙa buƙatar ga Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da basussukan cikin gida da na waje, tare da haɗin gwiwar kwamitocin kasafin kuɗi da kuɗaɗe, domin su nazarci shirin.

An buƙaci kwamitocin su gabatar da rahotonsu ga majalisar cikin mako guda.

A halin yanzu, buƙatar rancen na jiran nazari da amincewar Majalisar Dattawa kafin a iya ci gaba da matakan da suka dace.