Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ne ya karanta wasiƙar buƙatar shugaban ƙasar a zauren majalisar, inda Tinubu ya nemi izinin gwamnatin tarayya ta samo kuɗaɗen ta hanyoyin karɓar rance daga ƙasashen waje, ciki har da sayar da takardun bashin Eurobond.
A cikin wasiƙar, shugaban ƙasar ya bayyana cewa an riga an tanadi wannan rance a cikin dokar kasafin kuɗin shekarar 2026, wadda ta ƙunshi hanyoyin samun kuɗaɗe daga cikin gida da kuma ƙasashen waje.
Tinubu ya ce kuɗaɗen za su taimaka wajen aiwatar da ayyuka da shirye-shiryen da aka tanada a kasafin kuɗin shekarar 2026, musamman a fannonin tsaro, sufuri, noma, wutar lantarki, ilimi da kiwon lafiya.
