Tinubu ya ce ya kamata kamfen ɗin siyasa ya mayar da hankali kan muhimman batutuwan da za su inganta rayuwar al’umma da kuma ci gaban ƙasa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya jaddada cewa bambancin jam’iyya ko ra’ayin siyasa ba yana nufin cewa mutane su zama maƙiyan juna ba.
Ya kuma sake nanata aniyarsa ta tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana da adalci, tare da kira ga shugabannin siyasa da magoya bayansu da su gudanar da harkokinsu cikin lumana.
Haka kuma, Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su ɗauki matakan da suka dace kan duk wanda ya nemi tayar da zaune tsaye ko karya doka da oda.
A cikin sanarwar, shugaban ya ce wajibi ne a kare dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu daga duk wata barazana yayin gudanar da yaƙin neman zaɓe a sassan ƙasar.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani rashin ɗa’a daga ’yan siyasa da magoya bayansu ba, inda ya buƙaci jami’an tsaro su ɗauki tsauraran matakai kan ’yan bangar siyasa da ke ƙoƙarin haddasa fitina.
