Yankin Arewa na da masu rajistar zaɓe miliyan 56.01 daga cikin jimillar masu rajista miliyan 103.43 da ke faɗin Najeriya, lamarin da ya sa yankin ke da muhimmiyar rawa wajen tantance sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ana sa ran gwamnoni 31 da sauran manyan jiga-jigan APC za su halarci taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen. Jam’iyyar na fatan cin gajiyar abin da shugabanninta suka bayyana a matsayin ƙaruwa a goyon bayan masu ruwa da tsaki da masu kaɗa ƙuri’a a Arewacin Najeriya, domin tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen mai zuwa.
APC ta kuma sanya wa kanta burin tattara ƙuri’u miliyan 40 ta hanyar gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a daga tushe, musamman mata. Shugabannin jam’iyyar na nuna ƙwarin gwiwar cewa za su samu isasshen goyon baya domin Tinubu ya sake lashe zaɓe tare da samun wa’adi na biyu.
Sai dai jam’iyyun adawa sun nuna shakku kan wannan ƙwarin gwiwa ta APC, suna masu cewa matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa da matsalolin tsaro da ake fuskanta a sassa daban-daban na ƙasar na iya kawo cikas ga yunƙurin sake zaɓen shugaban ƙasar.
A nasu ɓangaren, masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, sun bayyana cewa ’yan Najeriya daga sassa daban-daban na ƙasar, da kuma mabiya addinai daban-daban, a shirye suke su kaɗa ƙuri’ar sauya gwamnati tare da kawar da APC daga karagar mulki.
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara matsowa, ana sa ran fafatawar siyasa za ta ƙara zafi, musamman a Arewacin Najeriya, inda yawan masu rajistar zaɓe ke sanya yankin cikin muhimman wuraren da jam’iyyun siyasa za su mayar da hankali wajen neman goyon baya.
