A lokacin da yake jawabi a wani taron yaƙin neman zaɓe a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, ranar Talata, Shettima ya ambaci Sule Lamido a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da ke tare da su.
“Wai ina maganar Jigawa, su wane ne Jigawa? Ga mu nan muna tare da Saminu Turaki da Ali Sa’adu B/Kudu da Muhammad Badaru Abubakar, dukkansu tsoffin gwamnonin jihar. Kai, har Alhaji Sule Lamido yana tare da mu,” in ji Shettima.
Kalaman sun haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan siyasa, inda wasu suka fara nuna shakku kan matsayar siyasar Sule Lamido, tare da zargin cewa yana aiki tare da jam’iyyar APC.
Sai dai jim kaɗan bayan kalaman mataimakin shugaban ƙasar, Lamido ya fito ya yi watsi da batun, yana mai cewa ba shi da wani dalilin komawa APC a halin yanzu.
A wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta DC Hausa, Lamido ya ce kamar yadda ya ƙi komawa APC a baya duk da kiraye-kirayen da manyan jam’iyyar suka yi masa, haka kuma babu wani dalili da zai sa ya koma cikinta a yanzu.
“Yadda a baya ban yi APC ba, duk da kiraye-kirayen da manyan jam’iyyar suka yi mini, ai yanzu babu wani dalilin da zai sa na yi APC,” in ji shi.
Lamido ya kuma danganta kalaman Shettima da wasan barkwanci da ke tsakanin al’ummomin Fulani da Kanuri.
