UNHCR ta ce kwararar waɗannan mutane na ƙara matsin lamba kan albarkatun Nijar, wadda tuni take ɗauke da ’yan gudun hijira da masu neman mafaka sama da 500,000, ciki har da kusan ’yan Nijeriya 327,500.
Haka kuma, wasu ɗaruruwan ’yan Nijeriya sun nemi mafaka a ƙasar Benin sakamakon matsalar tsaro.
Mafi yawan waɗanda suka isa Nijar a baya-bayan nan sun zauna ne a yankunan Diffa da Tahoua da ke kusa da iyakar ƙasar. UNHCR ta ce sama da mutum 23,000, waɗanda fiye da kashi biyu bisa uku daga cikinsu yara ne, sun isa yankin Diffa kaɗai tun farkon wannan shekara.
“Dubban ’yan gudun hijira da suka iso kwanan nan, da dama daga cikinsu yara ne, na fuskantar matsalolin rayuwa sakamakon ƙarancin abinci, tsaftataccen ruwa, matsuguni da muhimman hidimomi, yayin da tallafin jin ƙai ya yi ƙaranci matuƙa,” in ji kakakin UNHCR, Dominique Hyde, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.
Matsugunan wucin-gadi
Ta ce iyalai da dama na zaune ne a matsugunan wucin-gadi, yayin da mata ke yin tafiyar kilomita da dama a kowace rana domin samo ruwa.
Yawaitar mutanen da ke tserewa daga gidajensu na nuna irin tasirin da rikicin tsaro a arewacin Nijeriya ke yi ga sauran ƙasashen yankin.
A cikin shekaru goma da suka gabata, hare-haren Boko Haram, ƙungiyar Daesh da kuma ƙungiyoyin masu aikata laifuka sun tilasta wa miliyoyin mutane barin muhallansu.
Ƙungiyoyin agaji sun kuma bayar da rahoton ƙaruwar matsalolin tamowa, cututtukan numfashi da ƙarancin tsaftar muhalli a tsakanin mutanen da suka isa yankunan.
Haka kuma, matsalolin da suka shafi kare haƙƙin waɗannan mutane na ƙara ta'azzara. Kashi biyar cikin ɗari kawai na ’yan gudun hijirar da suka isa Nijar a bana ne aka yi wa rajista a hukumance, lamarin da ya sa da dama daga cikinsu ba su da takardun da ake buƙata domin samun tallafin jin ƙai da wasu hidimomin gwamnati.
UNHCR na neman tallafin dala miliyan 11.4 domin faɗaɗa ayyukan agajinta a Nijar, Nijeriya da Benin.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa dubban iyalai da rikici ya raba da muhallansu na iya rasa muhimman tallafe-tallafen jin ƙai idan ba a samar da ƙarin kuɗaɗen gudanar da ayyukan agaji ba.
