Da yake zantawa da gidan talabijin na gwamnatin Rasha mai suna Vesti, Ushakov ya bayyana cewa tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta gudana cikin nasara.

Kafofin yaɗa labaran Rasha sun yaɗa wani bidiyo da ke nuna Trump yana shiga ɗakin taron, inda ya nufi Putin tare da cewa: "Wannan abokina ne!"

A cewar Ushakov, yaƙin Ukraine ne babban batu da aka fi mayar da hankali a kai yayin ganawar, wadda ta ɗauki tsawon minti 35 zuwa 40.

Ya ƙara da cewa shugabannin sun tattauna kan dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen Amurka da Rasha.

Fadar Kremlin ta bayyana cewa babu wani daga cikin shugabannin biyu da ya yi wata muhimmiyar sanarwa bayan ganawar, yayin da suke shirin sake ganawa da Shugaban China, Xi Jinping, daga baya a wannan rana.