Matakin na daga cikin ƙoƙarin da Nijeriya ke yi na ƙara yawan ɗanyen man da take hakowa, jawo hankalin masu zuba jari da kuma ƙarfafa tsaron makamashi, kamar yadda wani babban jami'in hukumar ya bayyana a ranar Talata.
Hukumar ta ce amincewa da waɗannan ayyuka na cikin matakan da take ɗauka na gaggauta tantance buƙatun kamfanonin mai, domin rage jinkiri da kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.
Shugabar hukumar, Oritsemeyiwa Eyesan, ta ce ya zuwa yanzu a shekarar 2026, hukumar ta amince da tsare-tsaren raya filayen mai guda 39, sabbin ayyukan haƙo rijiyoyi 145 da kuma sake buɗe tsofaffin rijiyoyi 595.
Eyesan ta bayyana hakan ne a wani taron masana'antar mai da aka gudanar a jihar Legas. Mataimakin daraktan kula da tafkunan mai na hukumar, Ahmad Abdullahi, ne ya wakilce ta a taron.
Ta ce saurin amincewa da ayyukan zai taimaka wa kamfanonin mai wajen aiwatar da shirye-shiryensu na ƙara yawan man da suke samarwa da kuma inganta samar da makamashi a ƙasar.
Ta ƙara da cewa Nijeriya na da injinan haƙo mai sama da 100, inda 46 daga cikinsu ke aiki a wannan shekarar. Wannan adadi ya nuna ƙarin sama da kashi 300 idan aka kwatanta da shekarar 2021.
Haka kuma, Eyesan ta bayyana cewa kamfanonin da ke gudanar da binciken yanayin ƙasa ta hanyar amfani da na'urorin girgizar ƙasa (Seismic) sun zuba jarin sama da dala miliyan 100 a Nijeriya tun bayan fara aiwatar da dokar masana'antar man fetur ta ƙasar (Petroleum Industry Act), shekaru uku da suka gabata.
A cewarta, wannan jari ya taimaka wajen inganta bayanan binciken ƙasa da kuma ƙarfafa ƙoƙarin gano sabbin ma'adinan ɗanyen mai da iskar gas.
Hukumar NUPRC ta kuma bayyana cewa tana ci gaba da ɗaukar matakan yaƙi da satar ɗanyen mai a sassa daban-daban na ƙasar.
