Herzog ya fara tattaunawa da shugabannin jam'iyyun siyasa bayan sakamakon zaɓen da aka gudanar a makon da ya gabata ya nuna cewa babu wata jam'iyya da ta samu isassun kujeru a majalisar dokokin Isra'ila, wato Knesset, domin kafa gwamnati ita kaɗai.
Eisenkot zai samu kwanaki 28 domin ƙoƙarin kafa sabuwar gwamnati, tare da yiwuwar ƙara masa wasu kwanaki 14 idan ya buƙata.
Tsohon babban hafsan sojin Isra'ilan ya bayyana a shafinsa na X cewa lokaci ya yi da za a kafa gwamnatin haɗaka ta ƙasa, yana mai cewa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin an cimma wannan buri.
Jam'iyyar Likud ta Netanyahu da ƙawayenta masu tsattsauran ra'ayi sun samu kujeru 53 daga cikin kujeru 120 na majalisar Knesset.
A gefe guda kuma, jam'iyyar Yashar ta Eisenkot tare da wasu jam'iyyun adawa uku na Yahudawa sun samu kujeru 48.
Sai dai jam'iyyun haɗaka guda biyu da Larabawa ke jagoranta sun samu kujeru 19, sakamakon ƙaruwar yawan Larabawa da suka kaɗa ƙuri'a, lamarin da ya ƙara musu tasiri wajen yanke shawarar wanda zai kafa gwamnati.
Duk da haka, akwai wata jam'iyyar Yahudawa da ta sha alwashin cewa ba za ta shiga gwamnatin haɗaka da jam'iyyun Larabawa ba, wanda hakan ke ƙara rikitar da ƙoƙarin kafa sabuwar gwamnati.
A tsarin siyasar Isra'ila, kafa gwamnati na buƙatar samun goyon bayan akalla mambobi 61 daga cikin kujeru 120 na majalisar dokokin ƙasar.
