A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin ya wallafa a shafinsa na X, ya jaddada aniyarsa ta ganin an ci gaba da kyautata dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Takaddamar ta samo asali ne bayan katse watsa shirye-shirye kai tsaye a shafin YouTube na fadar shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, a daidai lokacin da Fani-Kayode ke shirin miƙa takardun shaidar kama aikinsa ga Shugaba Ramaphosa a birnin Tshwane.
Bayan katsewar watsa shirye-shiryen, Fani-Kayode ya zargi jami’an da ke kula da watsa taron da cire jawabinsa da gangan. Sai dai ya yaba wa Shugaba Ramaphosa bisa shiga tsakani bayan an sanar da shi abin da ya faru.
A martaninsa, Magwenya ya zargi Fani-Kayode da yin ƙarya kan zargin cewa Ramaphosa ya shiga tsakani domin warware matsalar.
Ofishin Jakadancin Najeriya ya bayyana kalaman Magwenya a matsayin tsokana da rashin dacewa da ƙa’idojin diflomasiyya, yana mai cewa ya kamata a warware irin wannan saɓani ta hanyar tattaunawa cikin lumana.
Duk da haka, ofishin jakadancin ya ce ya ɗauki batun a matsayin wanda aka rufe, tare da jinjina wa Shugaba Ramaphosa bisa umarnin da ya bayar na sakin cikakken bidiyon taron domin fayyace abin da ya faru.
