Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Hon. Nafiu Bala Gombe, ya yi maraba da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wanda ya soke shugabancin David Mark na jam’iyyar.

A ranar Alhamis ne kotun ta yanke hukuncin soke dukkan matakan da ɓangaren David Mark ya ɗauka a madadin jam’iyyar ADC.

Matakan da abin ya shafa sun haɗa da tsayar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.

Nafiu Gombe, wanda shi ne ya shigar da ƙarar, ya bayyana jin daɗinsa kan hukuncin, yana mai cewa tun da daɗewa yake fafutukar tabbatar da gaskiya a rikicin shugabancin jam’iyyar.

“Dama na jima ina magana a kan gaskiya, gaskiya, to ga shi yau gaskiyar ta yi halinta,” in ji shi.

Tun da farko dai, Nafiu Gombe ya gabatar da nasa ’yan takara a ƙarƙashin ɓangarensa na jam’iyyar.

Ya ce bayan hukuncin kotun, za su mayar da hankali wajen ci gaba da yaƙin neman zaɓe da tallata ’yan takararsu domin tunkarar babban zaɓen 2027.

“Yanzu za mu mayar da hankali wajen ci gaba da tallata ’yan takararmu domin tunkarar zaɓen 2027 da ke tafe,” in ji shi.