Ya ce saboda haka, INEC ba za ta dogara da bayanan da ke yawo a kafafen sada zumunta wajen aiwatar da umarnin kotu ba.

Farfesa Amupitan ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar.

Wannan na zuwa ne bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci INEC da ta gabatar da takardun tsayawar takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, waɗanda suka shafi takararsa a zaɓen gwamnan Jihar Legas na shekarar 1999 da kuma zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Haka kuma, kotun ta umarci Farfesa Amupitan da ya gurfana a gabanta domin ba da shaida a ƙarar da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta shigar kan Omoyele Sowore, dangane da wani rubutu da ya wallafa wanda ya shafi Shugaba Tinubu.

Sai dai Amupitan ya ce har zuwa lokacin da yake magana, INEC ba ta karɓi cikakkun umarnin kotun ba. Ya ƙara da cewa da zarar sun karɓe su, hukumar za ta ɗauki matakan da doka ta tanada kan lamarin.