Mazauna ƙauyen sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa maharan, waɗanda aka ruwaito sun iso a kan babura, sun kewaye ƙauyen tare da buɗe wuta kan mutanen garin.
A cewar mazauna yankin, maharan sun kewaye ƙauyen ne da nufin kai masa hari, lamarin da ya tilasta wa mutanen garin tashi tsaye domin kare kansu da al’ummarsu.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun isa ƙauyen ne a lokacin da wasu daga cikin mazauna yankin suka tafi gonakinsu domin girbe amfanin gona.
“Kafin mu ankara da abin da ke faruwa, ’yan bindigar sun riga sun kewaye ƙauyen daga kowane ɓangare, inda mutum uku ke kan kowane babur,” in ji mazaunin.
Ya ƙara da cewa mazauna ƙauyen sun fuskanci maharan ne domin kare kansu daga yiwuwar rasa matsugunansu da zama ’yan gudun hijira.
“Mun kashe kusan ’yan bindiga 30 a wannan artabu,” kamar yadda ya shaida wa Daily Trust.
A nata ɓangaren, rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa a shirye take ta tallafa wa mazauna ƙauyen wajen samar musu da kariya.
Sai dai har yanzu, ba a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata a artabun daga wata majiya mai zaman kanta ba.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da zama babban ƙalubale ga tsaro da zaman lafiyar al’ummomi a sassan Jihar Zamfara.
