Ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da ya gurfana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Gwamnati, wanda ke binciken tambayoyin da Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya ya gabatar dangane da bayanan kuɗaɗen NNPCL a lokacin jagorancinsa.

Da yake kare kansa, Kyari ya ce kamfanin ya yi ƙoƙarin aiwatar da manufofin da Majalisar Dokoki ta ƙasa ta tsara, lamarin da ya taimaka wajen jawo zuba jari da inganta harkokin tace man fetur domin amfanin ƙasar.

“Ina alfahari da cewa mun yi wa wannan ƙasa hidima yadda ya kamata. Ina biyayya ga ƙasata, kuma ban aikata wani abu da bai dace ba da gangan,” in ji shi.

Dangane da kuɗaɗen da aka biya Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS), Kyari ya ce kuɗaɗen rajista ne, yana mai bayyana bambancin da aka samu a bayanan a matsayin matsalar shigar da bayanai.

Ya kuma bayyana cewa naira biliyan 2.9 da ake magana a kai kuɗaɗe ne da doka ta tanadi biyan su.

Game da zargin kashe naira biliyan biyar wajen sauya sunan NNPCL, tsohon shugaban kamfanin ya ce Majalisar Dokoki ce ta amince da sauya sunan, kuma ba a kashe ko sisi wajen aiwatar da hakan ba.

Bayan kammala bayaninsa, Kyari ya miƙa rahotonsa ga kwamitin.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin ya ce an gabatar da tambayoyi kan batutuwa 23, amma ɗaya ko biyu ne kawai suka shafi tsohon shugaban NNPCL kai tsaye.

Ya ce za a rarraba rahoton ga mambobin kwamitin domin nazari, sannan za a iya gayyatar sauran waɗanda abin ya shafa da kuma Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya domin ƙarin bayani idan hakan ya zama dole.

“Mun karɓi uzurin da ka bayar kan rashin halartar zaman kwamitin da ya gabata, kuma za mu gudanar da nazarinmu bisa alkaluman da ke gabanmu,” in ji shugaban kwamitin.

Daga bisani, kwamitin ya sallami Kyari yayin da yake ci gaba da bincikensa.

Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Gwamnati ya fara binciken batun ne a watan Yunin 2025, bayan gano saɓani a bayanan kuɗaɗen NNPCL na shekarun 2017 zuwa 2023.

Alƙaluman da ake bincike a kansu sun haɗa da naira tiriliyan 103 da aka bayyana a matsayin kuɗaɗen da aka tara, da kuma naira tiriliyan 107 da ba su cikin kuɗaɗen shiga na yau da kullum.

Kwamitin ya sha nuna rashin gamsuwarsa da bayanan da kamfanin ya gabatar, yana mai buƙatar cikakken bayani kan yadda aka shigar da waɗannan alkaluma.

A watan Maris na 2026, kwamitin ya aika sammaci ga Kyari da wasu tsoffin jami'an kamfanin domin su yi karin bayani kan lamarin. Sai dai a watan Yunin shekarar, kwamitin ya bayar da umarnin kama shi bayan ya kasa bayyana a gabansa.

Duk da haka, tsoffin jami'an NNPCL sun ci gaba da musanta cewa an yi asarar kuɗaɗen, suna mai cewa zargin naira tiriliyan 210 ya samo asali ne daga rashin fayyace bayanan kuɗaɗen kamfanin yadda ya kamata.