KACRAN ta kuma yaba wa sabon shirin tsaro na shekaru biyar da gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar domin magance matsalar rashin tsaro da ƙasar ke fama da ita.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Hon. Muhammad Khalil Bello, ya fitar, ya ce KACRAN ta nazarci shirin, inda ta lura cewa ya ƙunshi matakan ƙarfafa rundunonin tsaro, amfani da fasahar zamani, inganta tattara bayanan sirri da kuma ɗaukar sabbin jami'an tsaro 78,000.
Sai dai ƙungiyar ta bayyana damuwa kan tsawon lokacin da aka ware domin cimma manufofin shirin, tana mai cewa al'ummomin da ke fama da hare-hare, garkuwa da mutane da kuma ƙaura daga gidajensu ba za su iya jira har tsawon shekaru biyar ba.
KACRAN ta yi iƙirarin cewa kashi 80 cikin 100 na matsalar tsaro a Najeriya na da alaƙa da matsalolin zamantakewa, kamar rikicin manoma da makiyaya, talauci, rashin aikin yi da jahilci, waɗanda a cewarta za a iya magance su ta hanyar sulhu da tattaunawa.
Ƙungiyar ta ce tana da wani tsarin samar da zaman lafiya cikin kwanaki 45, wanda ya haɗa da sasanci tsakanin manoma da makiyaya, samar da adalci ga waɗanda abin ya shafa, bunƙasa noma da kiwo, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma ƙarin tallafi ga shirye-shiryen raya yankunan da suka fi fama da matsalar rashin tsaro.
KACRAN ta bayyana cewa aiwatar da waɗannan matakai zai taimaka wajen magance tushen matsalar rashin tsaro tare da samar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.
