Jordan ta ɗauki wannan mataki ne bayan wani hari da aka kai wa wata coci a watan da ya gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum tara.
Mahukuntan Jordan sun bayyana cewa mutane uku da aka yanke wa hukuncin kisa kan harin mabiya ne na akidar tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci.
Ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi, ciki har da ƙungiyar IS mai ikirarin kafa daular Musulunci, sun daɗe suna amfani da manhajar Telegram wajen yaɗa bidiyoyi da sanarwarsu.
Sai dai wanda ya kafa manhajar Telegram ya taɓa bayyana cewa kamfanin ya ɗauki matakai fiye da yadda ake buƙata wajen sa ido da kuma takaita wallafa abubuwan da suka saɓa wa ƙa’idojin manhajar.
