Magatakardar Majalisar Dokokin Ƙasa, Kamoru Ogunlana, ne ya sanar da cimma matsayar a ranar Litinin, inda ya ce adadin jihohin da suka amince da gyaran ya zarce mafi ƙarancin ƙa’idar kundin tsarin mulkin ƙasar, wadda ke buƙatar amincewar aƙalla jihohi 24.

Ya ce an kammala tantance sahihancin ƙudurorin amincewar, kuma an shirya miƙa kudirin ga Shugaba Bola Tinubu domin sanya masa hannu.

Kudirin gyaran kundin tsarin mulkin na neman samar da tsarin doka da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yan sandansu da gudanar da ayyukansu da kansu.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar rashin tsaro ke ƙara ƙamari a sassan Nijeriya, ciki har da satar mutane domin neman kuɗin fansa, ayyukan ’yan bindiga, hare-haren makamai da rikice-rikicen al’umma.

Masu goyon bayan matakin na ganin cewa kafa rundunonin ’yan sandan jihohi zai inganta tattara bayanan sirri, ƙarfafa aikin tabbatar da tsaro a cikin al’umma da kuma ba da damar gaggauta mayar da martani ga barazanar tsaro.

Sai dai masu adawa da shirin sun nuna damuwarsu kan yiwuwar gwamnonin jihohi amfani da rundunonin ’yan sandan wajen cimma muradun siyasa.

Sun kuma nuna damuwa kan batutuwan samar da kuɗaɗe, ƙa’idojin ɗaukar ma’aikata, sa ido kan ayyukan jami’an tsaro, ɗora musu alhaki da kuma haɗin gwiwa da rundunar ’yan sandan tarayya.

Masu sukar shirin sun yi kira da a samar da tsauraran matakan kariya a kundin tsarin mulki domin tabbatar da cewa rundunonin ’yan sandan jihohi za su gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa da ’yancin kai, ba tare da katsalandan na siyasa ba.