Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar a cibiyar Chatham House da ke birnin Landan, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Kimpact Development Initiative.

Taken taron shi ne, “Zaɓen Nijeriya na 2027: Tafarkin Dimokuraɗiyya da Zaman Lafiyar Yankin Bayan Kaɗa Ƙuri'a.”

A cewar sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai kuma mai ba shugaban INEC shawara kan harkokin yaɗa labarai, Adedayo Oketola, ya fitar a Abuja, Amupitan ya ce gwajin zai kwaikwayi yadda zaɓen shugaban ƙasa zai gudana, domin tantance ingancin na'urar tantance masu zaɓe ta BVAS da kuma tsarin aika sakamakon zaɓe ta intanet.

Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa INEC ta bullo da sabbin matakan kariya na fasaha domin hana aika sakamakon rumfunan zaɓe marasa inganci, da kuma alkaluman da ke nuna an samu kaɗa ƙuri'a fiye da adadin masu zaɓen da aka yi wa rajista a rumfar.

Ya ce binciken da hukumar ta gudanar bayan zaɓen 2023 ya nuna cewa cibiyoyin tattara sakamako ne suka fi haddasa matsalolin gudanarwa da tattara sakamakon zaɓe, ba rumfunan zaɓe ba.

Amupitan ya bayyana cewa hukumar ta zaɓi inganta fasahar zaɓen da take amfani da ita a halin yanzu, maimakon bullo da sabuwar fasaha gaba ɗaya, saboda ƙarancin lokacin da ya rage kafin zaɓen 2027.

Dangane da matsalolin da na'urar BVAS ta fuskanta a zaɓen 2023, shugaban INEC ya ce hukumar na gina wuraren adana na'urorin masu tsarin sanyaya iska a jihohin ƙasar, domin kare su daga illar matsanancin zafi.

Ya ƙara da cewa hukumar ta sayi ƙarin na'urorin BVAS, tare da rage yawan masu zaɓen da za a iya tantancewa da kowace na'ura daga 1,250 zuwa 850.

Hukumar ta ce za a bai wa rumfunan zaɓen da ke da masu zaɓe fiye da 850 ƙarin na'urori domin sauƙaƙa aikin tantance masu kaɗa ƙuri'a.