Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, yayin wani taron tattaunawa da ma’aikatan hukumar na shiyyar Arewa ta Tsakiya domin duba shirye-shiryen gudanar da zaɓen 2027.
Amupitan ya ce an ɗauki matakan ne domin inganta jin daɗin ma’aikata, ƙarfafa ayyukan zaɓe da kuma tabbatar da gudanar da zaɓe cikin inganci. Ya ƙara da cewa zaɓen mai zuwa zai shafi masu rajistar katin zaɓe sama da miliyan 103 a rumfunan zaɓe 176,846 da ke faɗin ƙasar.
Ya bayyana cewa sabon tsarin albashin ma’aikatan hukumar, mai suna Consolidated Election Management Body Salary Structure (CEMBSS), wanda aka samar bayan INEC ta fice daga tsarin albashin ma’aikatan gwamnati na yau da kullum, ya fara aiki tun ranar 1 ga Janairun 2026.
Ya ce ana ci gaba da kammala shirye-shiryen samar da kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen aiwatar da sabon tsarin albashin.
Haka kuma, hukumar ta amince da ƙarin alawus-alawus na haɗari da gudanar da ayyukan zaɓe ga ma’aikatanta, yayin da kuɗaɗen gudanar da ofisoshinta na jihohi suka ƙaru da kashi 150 cikin 100 tun daga ranar 1 ga Yulin 2026.
Dangane da kayan aiki kuwa, Amupitan ya ce hukumar ta raba motocin ɗaukar kaya da na gudanar da ayyuka ga ofisoshinta na jihohi da ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa an sayo sababbin motoci ƙirar SUV guda 20 domin kwamishinonin zaɓe na jihohi, yayin da sakatarorin gudanarwa na hukumar su ma za su samu sababbin motoci domin ƙarfafa ayyukansu.
Sai dai shugaban INEC ya gargaɗi ma’aikatan cewa inganta jin daɗinsu ba zai zama dalilin sakaci wajen gudanar da ayyukansu ba, yana mai jaddada buƙatar bin ƙa’idojin aiki, rashin nuna bambancin siyasa da kuma jajircewa.
Ya umarci ma’aikatan hukumar da su dakatar da zuwa hutun shekara, tare da gargaɗin cewa sakaci, rashin zuwa aiki, nuna goyon baya ga ’yan siyasa ko wani ɓangare da kuma almundahana da kuɗaɗe za su jawo musu hukuncin ladabtarwa.
Amupitan ya kuma umarci kwamishinonin zaɓe na jihohi da sakatarorin gudanarwa da su ƙarfafa sa ido kan halartar ma’aikata da tabbatar da ɗaukar alhaki.
Ya ce hukumar ba za ta lamunci duk wani hali da zai iya kawo cikas ga sahihanci da amincin babban zaɓen 2027 ba.
