Hukumar ta ce har yanzu ba ta iya tabbatar da ko akwai sinadaran nukiliya a cibiyar ba, ko kuma ainihin inda suke.

IAEA ta kuma bayyana cewa hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran sun haifar da wani yanayi na musamman da ba a taɓa fuskanta ba.

Sai dai hukumar ta buƙaci gwamnatin Iran da ta ba jami'anta damar komawa cibiyoyin nukiliyar ƙasar domin gudanar da bincike da kuma ci gaba da sa ido kan ayyukan da ake gudanarwa a wuraren.

Tun bayan hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila na tsawon kwanaki 12 a watan Yunin bara, gwamnatin Tehran ba ta sake ba jami'an IAEA izinin komawa wasu daga cikin cibiyoyin nukiliyar da aka kai wa hari ba.

Hukumar ta buƙaci Iran da ta ɗauki matakan da suka dace domin bai wa jami'an bincikenta damar komawa muhimman cibiyoyin nukiliyar ƙasar.