Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwar Jihar karo na 42, wanda aka gudanar daga daren Lahadi zuwa safiyar Litinin.

Kwamishinan ya ce gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da biyan haƙƙin ’yan fansho da suka daɗe suna jiran kuɗaɗensu, tare da sauke nauyin biyan basukan da ta gada.

Ya ƙara da cewa shirin biyan kuɗaɗen zai gudana ne daga watan Nuwamba zuwa ƙarshen watan Afrilu, wanda ke nufin za a kammala biyan bashin wata guda kafin cikar wa'adin mulkin gwamnatin na farko.

Wakilinmu, Kamal Umar Kurna, ya ruwaito cewa gwamnatin Kano ta sake jaddada aniyarta ta biyan dukkan kuɗaɗen fansho da ake bin ta, a wani yunƙuri na inganta walwalar tsofaffin ma'aikatan gwamnati da tabbatar da sun samu haƙƙoƙinsu.