Wata sanarwa da mai bai wa gwamnan jihar, Bala Mohammed, shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar ranar Asabar, ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take, kuma za ta ci gaba har sai wani kwamitin bincike mai mutum 12 da aka kafa ya kammala aikinsa.
Sanarwar ta ce an kafa kwamitin ne domin gudanar da bincike kan zargin amfani da sarautar da sarkin ke riƙe da ita wajen aikata abubuwan da suka saɓa wa doka.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta samu korafe-korafe da dama daga shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki da kuma jami’an tsaro dangane da ayyukan sarkin.
A cewarta, waɗannan korafe-korafe sun haifar da damuwa a masarautar Lame, tare da tayar da hankalin al’umma da kuma barazana ga zaman lafiya.
Zarge-zargen da ake yi wa sarkin sun haɗa da tsoma baki a harkokin filaye, karɓar haraji ba bisa ƙa’ida ba da kuma kawo cikas ga ayyukan kamfanonin da ke haƙar ma’adanai.
Sanarwar ta ƙara da cewa Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Masarautun Gargajiya ta nemi sarkin ya yi bayani kan zarge-zargen da ake yi masa, amma ta ce bayanin da ya bayar a rubuce bai gamsar da ita ba.
Daga bisani ne gwamnatin ta yanke shawarar kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar zarge-zargen da ake yi wa sarkin.
