Gwamnan ya gabatar da kasafin ne a safiyar Laraba, yayin wani zama na musamman da majalisar ta gudanar a babban zaurenta da ke birnin Kano.

Da yake jawabi a gaban 'yan majalisar, Abba Yusuf ya ce an tsara kasafin ne domin bunƙasa muhimman fannoni da suka haɗa da ilimi, kiwon lafiya, noma da ayyukan raya birane da ƙauyuka.

Ya kuma bayyana cewa kasafin zai mayar da hankali wajen samar da hanyoyin dogaro da kai ga matasa da mata, domin inganta rayuwarsu da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da an aiwatar da kasafin yadda ya kamata, domin inganta rayuwar al'ummar Kano da kuma cika alkawuran da ta ɗauka.

Ya buƙaci 'yan majalisar da su gaggauta nazarin ƙudirin tare da amincewa da shi a kan lokaci, domin bai wa gwamnati damar fara aiwatar da ayyukan raya ƙasa tun daga farkon shekarar 2027.