A ƙarƙashin wannan shawara, ƙasashen da suka shirya haɗa tsarin kuɗinsu za su fara amfani da ECO tare da kuɗaɗen ƙasashensu, yayin da sauran ƙasashe za su iya shiga tsarin idan sun cika ƙa'idojin da ake buƙata.
Mahama ya bayyana hakan ne ranar Talata, yayin taron koli na Haɗin Kan Afirka ta Yamma da Zuba Jari (WAIIS) a birnin Freetown na Saliyo.
Ya ce ƙoƙarin fara amfani da kuɗin ya kwashe shekaru da dama yana fuskantar tsaiko, sakamakon sauyin yawan ƙasashen da ke cika ƙa'idojin daidaita tattalin arziki.
“Ina da tabbacin cewa wasu daga cikinku ba a ma haife su ba lokacin da muka fara magana kan ECO, wato kuɗin bai ɗaya na Afirka ta Yamma,” in ji shi.
Sauyin yawan ƙasashen da suka cika sharuddan
Mahama ya tuna cewa yawan ƙasashen da suka cika sharuddan ya riƙa sauyawa tsakanin biyu, biyar, uku da bakwai. Wannan ne ya sa aka kasa samun dukkan ƙasashe 15 na Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) sun cika sharuddan da ake buƙata kafin fara amfani da kuɗin.
Ya ce shi da Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio, sun gabatar da shawara a wani taron ƙolin ECOWAS da ya gabata domin warware wannan matsala, ta hanyar bai wa ƙasashen da suka shirya damar fara haɗa tsarin kuɗinsu.
A ƙarƙashin tsarin, ECO zai sauƙaƙa biyan kuɗin cinikayya tsakanin ƙasashen da suka shiga cikinsa ba tare da sai an bi ta dalar Amurka ba, yayin da kuɗaɗen ƙasashen za su ci gaba da kasancewa a amfani.
Shugaban na Ghana ya kuma bayyana ƙarancin ababen more rayuwa na sufuri da jigilar kayayyaki a matsayin babban cikas ga faɗaɗa cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka, duk da ci gaban da aka samu ƙarƙashin Yarjejeniyar Cinikayya Marar Shinge ta Nahiyar Afirka (AfCFTA).
Ya ce cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka ta ƙaru daga kusan kashi 11 cikin 100 a lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar AfCFTA zuwa kusan kashi 15 cikin 100.
Sai dai ya ce wannan ƙididdiga ba ta kai matsayin cinikayya tsakanin ƙasashen Tarayyar Turai ba, inda take tsakanin kashi 50 zuwa 60 cikin 100.
“Amma babban cikas ɗin shi ne harkar sufuri da jigilar kayayyaki. Shin muna da tashoshin jiragen ruwa? Muna da layukan dogo? Muna da hanyoyi?” in ji shi.
Jinkirin aiwatar da manyan ayyukan haɗin gwiwar yankin
Mahama ya kawo aikin titin Lagos zuwa Abidjan, wanda aka daɗe ana jinkirin aiwatarwa, a matsayin misalin yadda ake tafiyar hawainiya wajen bunƙasa ababen more rayuwa a yankin.
Ya tuna cewa an fara gabatar da aikin ne a ƙarshen shekarun 1990, lokacin da yake ƙaramin minista.
“Yau shekaruna sun kusa 70, amma har yanzu aikin titin Abidjan zuwa Lagos yana kan takarda,” in ji shi, yana mai cewa wannan jinkiri ya nuna cewa haɗin kan yankin bai wuce buri da maganganu ba.
Ya buƙaci shugabannin Afirka ta Yamma su wuce matakin sanar da manufofi kawai, su hanzarta aiwatar da ayyukan samar da ababen more rayuwa da za su inganta zirga-zirgar mutane da kayayyaki a yankin.
Mahama ya kuma yi kira da a samar da ingantaccen tsarin hanyoyin mota na bai ɗaya, da kafa wuraren binciken iyakoki na bai ɗaya, tare da kawar da shingayen binciken jami'an tsaro da ba su da muhimmanci, domin sauƙaƙa cinikayya tsakanin ƙasashen yankin.
Ya ce kammala aikin titin Lagos zuwa Abidjan zai zama ginshiƙi wajen faɗaɗa hanyoyin sufuri na yankin zuwa Dakar, tare da ƙarfafa haɗin kan tattalin arzikin Afirka ta Yamma.
