Shugaban kamfanin Smart Innovation Ghana Limited, Dakta Sylvester Akpah, ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Accra ya shirya.

Ya ce ana shigo da sinadarin mercury cikin Ghana ta hanyoyin da ba a tantance ba, kuma ƙananan masu haƙar ma’adinai ne suka fi amfani da shi.

A cewarsa, sama da mutane miliyan biyu da rabi ne ke dogaro kai tsaye ko a kaikaice da ƙananan sana’ar haƙar ma’adinai domin samun abin masarufi, lamarin da ya sa amfani da mercury ba bisa ƙa’ida ba ke ƙara zama babban abin damuwa.

Dakta Akpah ya ce gurɓatar da sinadarin ke haifarwa ta fi shafar al’ummomin da ke haƙar ma’adinai a yankunan Western, Ashanti, Eastern da Central na Ghana, inda wasu koguna suka riga suka gurɓace.

Ya kuma bayyana garin Tarkwa da yankunan da ke maƙwabtaka da shi a matsayin wuraren da ke fuskantar matsanancin matsin lamba daga gurɓatar muhalli, yana mai cewa hakan na barazana ga samun tsaftataccen ruwan sha.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da shigo da mercury cikin ƙasar ta hanyoyin da ba su dace ba, duk da matakan tsaro da ake da su a tashoshin jiragen ruwa.

Dakta Akpah ya kuma nuna cewa rashin ingantacciyar hukumar da ke kula da amfani da mercury da sauran hanyoyin sa ido a harkar haƙar ma’adinai na kawo cikas ga ƙoƙarin shawo kan matsalar.

Ya ce masu haƙar ma’adinai da mutanen da ke zaune kusa da wuraren haƙar na fuskantar haɗarin kamuwa da sinadarin saboda amfani da shi a kai a kai wajen sarrafa zinare. Wannan na iya janyo illa ga ƙoda da huhu da kuma ƙwaƙwalwa.

Ya yi kira da a ƙarfafa aiwatar da dokokin da ake da su, tare da samar da wasu fasahohi da za su rage amfani da mercury, kafin daga bisani a daina amfani da shi gaba ɗaya wajen haƙar ma’adinai.

Dakta Akpah ya ce akwai wasu fasahohin fitar da zinare da za su iya maye gurbin mercury, sai dai amfani da su bai yaɗu ba, duk da jarin da ake zubawa wajen shigo da kayan aikin.

Ya kuma bayyana cewa Ghana ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Minamata kan sinadarin Mercury, wadda aka ƙulla domin kare lafiyar bil’adama da muhalli daga illolin wannan sinadari. Sai dai ya ce har yanzu akwai ƙalubale wajen aiwatar da yarjejeniyar a ƙasar.

A nasa ɓangaren, Farfesa Daniel Nukpezah, na Sashen Nazarin Muhalli da Shara a Jami’ar Ghana, ya ce matsalar gurɓatar muhalli da mercury na buƙatar ƙarin sa ido da ingantattun tsare-tsaren gudanarwa.

Ya bayyana mercury a matsayin wani ƙarfe mai guba da zai iya yaɗuwa a cikin muhalli ta iska da ruwa da ƙasa, tare da shiga jikin halittu masu rai.

Farfesan ya ce a wasu yanayin ruwa, ana iya sauya sinadarin mercury zuwa wani nau’in guba da ake kira methylmercury, wanda kan taru a jikin kifaye, daga nan kuma ya shiga cikin abincin da mutane ke ci.

Ya ce ƙananan halittu da ke cikin ruwa na iya shan wannan sinadari, sannan ya riƙa ƙaruwa a jikin kifaye yayin da manyan kifaye ke cin ƙananansu.

A cewarsa, hakan na ƙara haɗarin da mutane ke fuskanta ta hanyar cin kifayen da suka gurɓace.

Farfesa Nukpezah ya ce mutum na iya shiga haɗarin kamuwa da sinadarin ta hanyar shaƙar gurɓatacciyar iska, shan ko amfani da gurɓataccen ruwa, cin kifin da ya gurɓace, ko kuma ta hanyar taɓa gurɓatacciyar ƙasa da kuma aiki a wuraren haƙar ma’adinai.

Ya bayyana ƙananan sana’o’in haƙar ma’adinai a matsayin ɗaya daga cikin manyan hanyoyin gurɓatar muhalli da mercury a Ghana, saboda masu haƙar ma’adinan na amfani da sinadarin wajen raba zinare da duwatsun da ake haƙowa.