Binciken ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne ƙarƙashin wani shiri na sirri mai suna “VOLIA”, kalmar Ukraine da ke nufin ’yanci da ƙudirin kaiwa ga nasara, wanda wani janar na rundunar sojin Faransa ke jagoranta.
Rahoton ya ce sojojin Faransa da ke cikin shirin ba sa shiga fagen yaƙi kai tsaye, sai dai suna taimakawa wajen horas da sojojin Ukraine da kuma gyara wasu manyan makamai, da suka haɗa da manyan bindigogin Caesar, jiragen yaƙi da makamai masu linzami.
Haka kuma, binciken ya nuna cewa ana amfani da sansanin horas da sojojin Faransa da ke ƙasar Poland wajen shirya wasu daga cikin jami’an kafin a tura su Ukraine, domin ɓoye ainihin ayyukan da za su gudanar.
Sai dai wannan mataki ya jawo tambayoyi kan yadda gwamnatin Faransa ke gudanar da ayyukan sojinta a ƙasashen waje, musamman ganin cewa ba a bai wa majalisar dokokin ƙasar cikakken bayani kan shirin ba.
Wannan bankado sirrin na zuwa ne yayin da yaƙin Rasha da Ukraine ke ci gaba, lamarin da ka iya ƙara tayar da hankalin Moscow tare da zafafa muhawara kan irin rawar da ƙasashen Yamma ke takawa wajen taimaka wa Ukraine a yaƙin.
