Ma’aikatar Harkokin Wajen Chadi ta shaida wa BBC cewa za ta ƙara tsaurara matakan tsaro a kan iyakokinta, tare da ba wa mutanen da aka tabbatar ’yan ƙasar Chadi ne kaɗai damar komawa ƙasar.
“Za a ba ’yan ƙasar Chadi da aka tantance damar komawa gida, yayin da za a duba sauran shari’o’i daban-daban,” kamar yadda gwamnatin ta shaida wa BBC.
A makon da ya gabata ne hukumomin Nijar suka umarci al’ummar Larabawan Mahamid da ke ƙasar da su fice kafin ranar 31 ga Disamba, 2026.
Dubban Larabawan Mahamid ne ke zaune a Nijar, musamman a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Da dama daga cikinsu sun shafe shekaru masu yawa a Nijar, inda iyalansu na farko suka fara ƙaura zuwa ƙasar daga Chadi da Sudan tun a shekarun 1970.
Hukumomin Nijar ba su bayyana inda suke sa ran al’ummar za su nufa bayan ficewarsu daga ƙasar ba.
Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Chadi ta shaida wa BBC cewa ba za a ɗauki mutanen a matsayin ’yan ƙasar Chadi kai tsaye ba saboda kasancewarsu Larabawa Mahamid.
“Larabawan da ake magana a kansu ’yan Nijar ne. An haife su a Nijar, sun taso kuma sun yi rayuwarsu a can, kuma tushensu yana cikin ƙasar. Kasancewarsu membobin wata al’umma ko ƙabila ba hujja ba ce da ke tabbatar da cewa su ’yan ƙasar Chadi ne,” a cewar gwamnatin Chadi.
