Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin da ke mulki da hannu a abin da ya kira wani yunƙuri na raunana jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da kawo cikas ga takararsa ta shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin mayar da martani kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wanda ya soke shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark tare da rushe matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da tsarin da ya samar da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, Daraktan Sadarwa da Dabarun Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Atiku na ADC, ya fitar, Atiku ya ce lokacin da aka yanke hukuncin na da matuƙar muhimmanci, kasancewar ya zo ne kwana guda bayan dubban magoya bayansa sun tarbe shi a jihar Sakkwato yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.
Atiku ya ce taron na Sakkwato ya nuna cewa al’ummar ƙasar na buƙatar sauyi, kuma suna da fata kan alƙawarin da ya yi na dawo da sauƙin rayuwa.
Ya ce: “Al’ummar Sakkwato sun fito ne dubbansu saboda suna buƙatar sauyi, kuma sun yi imani da alƙawarinmu na dawo da sauƙin rayuwa. Abin da muka gani a Sakkwato mafari ne kawai. Al’ummar Kebbi ma za su bayyana ra’ayinsu, haka kuma sauran ’yan Najeriya yayin da yaƙin neman zaɓenmu ke ci gaba.”
Atiku ya kuma ce ba zai dakatar da yaƙin neman zaɓensa ba duk da hukuncin kotun, yana mai cewa gangamin zai ci gaba a faɗin jihohin Najeriya 36.
Ya bayyana cewa zai ƙalubalanci hukuncin a Kotun Ɗaukaka Ƙara, yana mai cewa akwai wasu batutuwan shari’a da ya kamata a sake dubawa.
Hukuncin kotun dai ya biyo bayan ƙarar da Nafiu Bala Gombe, tsohon Mataimakin Shugaban ADC na Arewa maso Gabas, ya shigar kan halaccin shugabancin David Mark da matakan da suka samar da shi.
Sai dai har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, hukuncin kotun na nan daram, yayin da ake jiran matakin ɗaukaka ƙarar da Atiku da jam’iyyar ADC suka ce za su ɗauka.
