Ƴan banga daga ƙauyen Zoma a karamar hukumar Bukkuyum sun yi wa ƴan bindigar kwantan ɓauna lokacin da suke wucewa ta wani ƙauye ranar Alhamis, bayan sace mutane da dama a garin Gummi, in ji majiyoyin.

"Ƴan banga sun samu damar kashe 44 daga cikin ƴanbindigar... mun kuma rasa ƴan banga tara a bata-kashin," kamar yadda wani mazaunin garin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa an kashe wani gungun ɗan bindiga mai suna Jiji, wanda ya jagoranci sace mutane a ƙauyen.

Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yamma da ke fama da matsalar ƴanbindiga waɗanda ke garkuwa domin neman kuɗin fansa da kuma sace dabbobi.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki, wanda ya ce ya jawo asarar kusan kashi 40 cikin 100 na mambobin ƙungiyar masu sana’ar yin burodi ta Najeriya, wato Premium Breadmakers Association of Nigeria, cikin shekaru biyu kacal.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Bauchi, Atiku ya ce durƙushewar masana’antun yin burodi da dama na nuna irin matsin tattalin arziki da tsadar makamashi da ‘yan kasuwa ke fuskanta, lamarin da ke tilasta wa kamfanoni rufe ƙofofinsu tare da ƙara tsadar kayan masarufi.

Ya bayyana cewa ya je Bauchi ne domin ci gaba da yaƙin neman zaɓensa, inda ya yi alƙawarin samar da sauƙin rayuwa tare da jajanta wa ‘yan Najeriya da ke fuskantar matsin tattalin arziki sakamakon manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Atiku ya ce asarar kusan kashi 40 na mambobin ƙungiyar masu yin burodi na nuna irin illar da tabarbarewar tattalin arziki ke yi ga ‘yan kasuwa da sauran al’umma.

Ya ƙara da cewa tuni ake ganin tasirin matsalar a sassa daban-daban na ƙasar, inda gidajen burodi da dama suka rufe, mutane suka rasa ayyukansu, yayin da farashin burodi ke ƙara tashi.

A cewarsa, wannan ƙarin farashi na ƙara wa miliyoyin iyalai da ke dogaro da burodi a matsayin abincin yau da kullum wahalar ciyar da iyalansu.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakan magance tsadar makamashi da kuma rashin samun rancen kuɗi cikin sauƙi, waɗanda ya ce na daga cikin manyan matsalolin da ke tilasta wa masana’antu da kasuwanni rufe ayyukansu.

Ya ce yayin da farashin samar da kayayyaki ke ƙaruwa, ma’aikata na ci gaba da rasa ayyukansu, yayin da talakawa ke fuskantar ƙarin tsadar kayan abinci.

Atiku ya sake jaddada aniyarsa ta gina tattalin arzikin da zai mayar da hankali kan samar da kayayyaki a cikin gida, kare ayyukan yi da kuma sauƙaƙa rayuwar al’ummar Najeriya.