Atiku, wanda ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana hakan ne bayan wani rahoto da gidauniyar Foundation for Investigative Journalism (FIJ) ta wallafa, bisa bayanan cibiyar Centre for Democracy and Development (CDD) na watan Oktoba.
Rahoton ya nuna cewa an kashe mutane 638 sakamakon hare-haren rashin tsaro a cikin watan Oktoba, inda jihohin Arewa maso Gabashin Nijeriya suka fi fama da asarar rayuka, da mutane 409 da aka kashe.
Haka kuma, bayanan sun nuna cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon matsalolin tsaro ya kai 640 a watan Oktoba, idan aka kwatanta da 396 da suka mutu a watan Satumba.
A gefe guda kuma, Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa kusan mutane 64,000 ne suka tsere daga hare-hare da tashe-tashen hankula a Arewacin Nijeriya zuwa ƙasar Nijar tun farkon shekarar 2026. Haka kuma, ɗaruruwan mutane sun tsere zuwa Benin domin neman mafaka.
A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC, ya fitar, Atiku ya ce waɗannan alkaluma na nuna girman matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Ya bayyana cewa kashe-kashen na jefa iyalai cikin ƙunci tare da tilasta wa al'ummomi barin gidajensu saboda rashin tsaro. Ya kuma ce bai kamata 'yan Nijeriya su riƙa tsallaka iyakokin ƙasarsu zuwa wasu ƙasashe domin neman mafaka ba.
Atiku ya buƙaci gwamnatin Tinubu ta mayar da kare rayuka da dukiyoyin al'umma a matsayin babban abin da ta sa a gaba, tare da ƙarfafa ayyukan jami'an tsaro a yankunan da hare-hare suka fi ƙamari da kuma tallafa wa mutanen da suka rasa matsugunansu.
Haka kuma, ya buƙaci Nijeriya ta ƙara haɗin gwiwa da ƙasashen maƙota da ƙungiyoyin agaji domin taimaka wa mutanen da suka tsere daga gidajensu.
Kazalika, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce 'yan Nijeriya na buƙatar cikakken bayani kan matakan da gwamnati ke ɗauka domin kawo ƙarshen kashe-kashe da dawo da zaman lafiya.
Ya kuma buƙaci Shugaba Tinubu ya ɗauki alhakin tabarɓarewar tsaro, yana mai cewa kare rayuka da dukiyoyin al'umma shi ne babban nauyin da ke rataya a wuyan kowace gwamnati
