Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) da ta fayyace tsarin fasahar AI da take shirin amfani da shi wajen gudanar da zaɓen 2027, tare da gudanar da bincike mai zaman kansa a kansa.
Atiku, ta bakin Daraktan Sadarwa da Dabarun Yaɗa Labaransa, Phrank Shaibu, ya ce ya aika da koke ga shugaban INEC a madadin Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) da sauran masu ruwa da tsaki.
A cikin koken, ya buƙaci hukumar da ta bayyana yadda tsarin ke aiki, ta gudanar da bincike mai zaman kansa a kansa, tare da samar da ƙa'idojin sa ido na ɗan'adam.
Wannan buƙata na zuwa ne bayan INEC ta sanar da shirin haɗa fasahar AI da tsarin sarrafa takardu ta na'ura wajen tantance sakamakon zaɓe a matakin mazaɓu, ta hanyar tsarin Data Verification and Authentication System (DIVAS) da kuma shafin INEC Result Viewing (IReV).
Atiku ya yi gargaɗin cewa idan ba a samar da isassun matakan kariya ba, fasahar na iya jinkirta sakamakon zaɓe na gaskiya ko nuna shi a matsayin wanda ake zargi da matsala sakamakon rashin ingancin hoton takarda, rubutun hannu ko wasu matsalolin fasaha.
Ya buƙaci INEC da ta bayyana lambar sirrin tsarin AI (source code), bayanan da aka yi amfani da su wajen horas da shi, ƙa'idojin gudanar da aikinsa, da kuma sunayen waɗanda suka ƙirƙire shi da kamfanonin fasahar da ke da hannu a aikin.
Haka kuma, ya buƙaci ƙwararru kan tsaron intanet masu zaman kansu, wakilan jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyin fararen-hula su gudanar da bincike kan tsarin kafin atisayen gwajin tantance masu kaɗa ƙuri'a a faɗin ƙasar da aka shirya gudanarwa ranar 28 ga Nuwamban 2026.
Atiku ya jaddada cewa ya kamata fasahar AI ta kasance kayan aiki na taimakawa wajen gudanar da ayyukan zaɓe ƙarƙashin kulawar ɗan'adam, yana mai gargaɗin cewa bai kamata a ba ta ikon sauya sakamakon zaɓe, goge shi ko hana shigar da shi ba.
Ya kuma buƙaci INEC da ta samar da tsari na musamman na sake duba sakamakon da na'urar ta nuna yana da matsala, tare da bai wa jam'iyyun siyasa damar sa ido kan yadda ake shigar da sakamakon zaɓe a kan lokaci.
Kazalika, Atiku ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta gayyaci jami'an INEC domin su yi bayani kan matakan kariya da tsarin binciken fasahar.
Ya kuma buƙaci masu sa ido kan zaɓe da su gudanar da bincike sosai kan yadda ake shigar da sakamakon zaɓe ta hanyar na'ura.
Atiku ya ce ya kamata 'yan Najeriya su samu damar tabbatar da cewa sakamakon da aka tattara a rumfunan zaɓe ya yi daidai da wanda aka shigar a shafukan hukumar na intanet.
