Ƙasashen da suka amince da shirin sun haɗa da Jamus, Austria, Netherlands, Denmark da Girka. Sun bayyana cewa shirin mayar da baƙin hauren zai shafi mutanen da suka gaza samun nasara a ƙoƙarinsu na ƙalubalantar hukuncin ƙin amincewa da buƙatarsu ta neman mafaka a gaban kotu.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da ƙasashen suka fitar, sun ce yarjejeniyar da suka cimma da Rwanda za ta fara aiki nan take, inda ƙasashen za su ɗauki nauyin kuɗaɗen kwashe mutanen da kuma jigilar su zuwa ƙasar da ke Gabashin Afirka.
Mahukuntan ƙasashen na fatan mayar da aƙalla mutane 100 zuwa Rwanda a matakin farko, a farkon shekarar 2027, domin gwada tasirin shirin.
Ƙarƙashin wannan tsari, za a bai wa mutanen da aka mayar Rwanda damar zaɓar ci gaba da zama a ƙasar ko kuma komawa ƙasashensu na asali bayan shafe wasu watanni a can.
Ba kamar makamanciyar yarjejeniyar da gwamnatin Burtaniya ta kulla da Rwanda ko kuma yarjejeniyar da Italiya ta cimma da Albania ba, wannan sabon shiri ba zai shafi mutanen da har yanzu ake nazarin buƙatunsu na neman mafaka ba.
