An gudanar da bikin rantsar da alƙalan ne a ranar Litinin a shelkwatar Hukumar Manyan Alƙalai da Lauyoyi ta Najeriya (Body of Benchers Complex), da ke Abuja.

Alƙalan da aka rantsar sun haɗa da guda 138 waɗanda suka taɓa gudanar da irin wannan aiki a baya, da kuma sabbi 237 da aka zaɓo daga kotuna da hukumomin shari’a daban-daban a faɗin ƙasar.

Da take jawabi a wajen taron, Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta bayyana rantsar da alƙalan a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa dimokuraɗiyyar ƙasar.

Ta ce ingancin zaɓe bai taƙaita ga jefa ƙuri’a kawai ba, domin tabbatar da adalci da kuma sauraron ƙararrakin zaɓe cikin lokaci na da matuƙar muhimmanci wajen kare haƙƙin ’yan ƙasa.

Ta ƙara da cewa bangaren shari’a na da alhakin tabbatar da fifikon kundin tsarin mulki, bin doka da oda, da kuma ƙarfafa amincewar al’umma ga tsarin dimokuraɗiyya.

Haka kuma, ta gargaɗi alƙalan da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, adalci da riƙon amana, tana mai cewa al’umma na sa ido kan yadda za su gudanar da wannan muhimmin aiki.

A ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya, Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ce ke da ikon kafa kotunan sauraron ƙararrakin zaɓe domin yanke hukunci kan takaddamar zaɓukan gwamnoni, da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa da majalisun dokokin jihohi.

Rantsar da alƙalan na daga cikin shirye-shiryen bangaren shari’a na tunkarar ƙararraki da ka iya tasowa sakamakon babban zaɓen shekarar 2027.