Matakin ya kawo ƙarshen shekaru 33 na jagorancin Huang a kamfanin, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa fasahar ƙwaƙƙwaran basirar na'ura (AI).

Rahotanni sun ce Huang, mai shekaru 63, ya kuma sauka daga muƙaminsa na mamba a majalisar gudanarwar kamfanin, sai dai ba a bayyana dalilin matakin ba.

Ficewarsa daga muƙamin ya zo ne a wani muhimmin lokaci ga masana'antar fasahar AI, inda Nvidia ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da na'urorin sarrafa bayanai da ake amfani da su wajen haɓaka wannan fasaha.

Haka kuma, labarin ya yi iƙirarin cewa hannayen jarin kamfanin sun fuskanci faɗuwa a kasuwar hada-hadar hannayen jari, inda darajarsu ta ragu da kashi 13 cikin ɗari a farkon cinikin hannayen jarin a Wall Street, kafin daga bisani ta samu ɗan farfaɗowa.

A wani ɓangare na labarin, an ambaci zarge-zargen da ake yi wa Huang kan wata alaƙar soyayya da wata mata a wajen aurensa da matarsa, Lori Huang, wadda suka shafe sama da shekaru 40 tare.

Haka kuma, labarin ya danganta lamarin da zargin alaƙar matar da China da kuma batun leƙen asiri, wanda ya jawo hankalin 'yan majalisar dokokin Amurka.

An kuma ruwaito cewa Huang ya amince zai ba da shaida a gaban Majalisar Dokokin Amurka kafin ranar 26 ga Nuwamba, kamar yadda Brian Mast, shugaban Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar Wakilai, ya bayyana.

Sakataren Harkokin Ciniki na Amurka, Howard Lutnick, shi ma ana sa ran zai bayar da shaida a gaban majalisar, kamar yadda kafafen yaɗa labaran Amurka suka ruwaito.

'Yan majalisar dokokin Amurka na neman gwamnati ta yi karin bayani kan abin da ta sani game da zargin alaƙar matar da China da kuma yiwuwar leƙen asiri.